Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi Allah-wadai da sace ‘yan mata 25 daga Makarantar sakandare ta gwamnati, da ke a Maga, a karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi, tare da kiran addu’a ga wadanda abin ya shafa.
Moore ya ce duk da har yanzu ba su samu cikakken bayani ba kan wannan mummunan hari, amma ya bayyana cewa yana kyautata zaton ya faru ne a wani yanki na Kiristoci a Arewacin Nijeriya, kuma ya bukaci hukumomi su dauki kwakkwaran mataki.
An kai harin ne da safiyar ranar Litinin, inda ‘yan bindiga suka shiga makarantar da makamai, suka hallaka mataimakin shugaban makarantar, tare da raunata wasu ma’aikata, sannan suka sace ‘yan mata 25 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



