An yi hatsaniya a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja sakamakon yunkurin bangarori biyu na jam’iyyar su gudanar da zaman nasu a rana ɗaya, abin da ya haifar da rikici a harabar Wadata Plaza.
Rahotanni sun bayyana cewa sakataren jam’iyyar na bangaren Wike, Samuel Anyanwu, ya isa sakatariyar tare da magoya bayansa, sai daga baya kuma mambobin bangaren Taminu Turaki suka iso amma ba a bari suka shiga ba.
Wasu gwamnoni biyu daga bangaren Turaki sun tilasta shiga, amma da sauran ’ya’yan bangaren suka yi ƙoƙarin bi, jami’an tsaro suka harba bindiga da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su.
Lamarin ya haifar da firgici inda mutane suka watse domin neman tsira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A jawabinsa kafin zuwan ɗayan bangaren, Anyanwu ya ce ƙarin tsaro da aka gani al’ada ce domin kaucewa tashin hankali, kana ya bayyana shirin bangarensa na gudanar da zaman BoT da NEC.



