Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla 100,000 cikin rundunonin tsaro domin ƙarfafa tsaron ƙasar da ya yi rauni.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan matakin ya biyo bayan kudirin da Sanata Abdullahi Yahaya na Kebbi ta Arewa ya gabatar, inda ya ce matsalar tsaro ta kai wani yanayi mai tayar da hankali da ke bukatar gaggawar daukar matakin kasa.
Sanatoci irin su Abdul Ningi da Aminu Tambuwal sun ce lamarin barazana ce ga makomar kasa, suna kira ga ‘yan majalisa su guji siyasantar da batun, yayin da tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya nuna takaicinsa cewa duk da kudaden tsaro masu yawa, hare-hare da sace-sace na ci-gaba.
Majalisar ta kuma kafa kwamiti na wucin-gadi domin binciken yadda aka yi amfani da kudaden shirin “Safe School” duk da cewa makarantun ƙasar na kara zama cikin hadari, musamman bayan sace dalibai a Kebbi.



