Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a duk faɗin Yammacin Afrika, kamar yadda shugaban hukumar, Omar Touray, ya bayyana a wajen kaddamar da shirin “Regional Partnership for Democracy” a Abuja.
Wakilinsa, Abdel-Fatau Musah, ya ce dimokuradiyya na cikin tsananin barazana a yankin, yana yaba wa Nijeriya, Ghana, Senegal da Cabo Verde bisa tsayuwa kan tsarin jam’iyyu da dama, tare da nanata cewa matsalar Nijeriya na iya shafar makomar yankin baki ɗaya.
Musah ya yi kira ga ƙasashen Yammacin Afrika su sake nazarin wa’adin shekara huɗu na shugabanci saboda rashin wadatar da yake yi wajen aiwatar da manyan shirye-shirye da kuma gina dimokuradiyya mai ɗorewa.
Haka kuma, ya bayyana kalubalen da ke barazana ga tsarin mulki a yankin, ciki har da juyin mulki, amfani da kotu wajen karkatar da doka, da kuma hana jam’iyyun adawa damar shiga siyasa, yana mai cewa wa’adin shekara huɗu ba ya wadatarwa ga ƙasashe irin su Nijeriya da Ghana wajen magance matsalolin ci-gaba.



