Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya sanar da jinkirta komawarsa jam’iyyar APC sakamakon sace ‘yan makaranta da ‘yan bindiga suka yi a Kebbi.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun gwamnan, Kefas ya bayyana cewa gabatar da wani lamarin siyasa a daidai lokacin da kasa ke cikin irin wannan yanayi na sabon jimamin matsalar tsaro ba abu ne da ya dace ba.
Jaridar Punch ta ruwaito sakataren jam’iyyar APC na Nijeriya Felix Morka, na bayyana cewa an dage bikin tarbar gwamnan zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba.
A baya dai an tsara ficewar gwamna Kefas daga jam’iyyar hamayya ta PDP, tare da komawa APC mai mulkin Nijeriya a ranar Laraba 19 ga watan Nuwamban 2025.



