Kungiyar kare hakin bil’adama ta Amnesty International ta gargadi cewa hare-haren ’yan bindiga da ƙungiyoyin ta’addanci suna tura Jihar Katsina zuwa ga mummunan bala’in jin-kai, yayin da dubban al’ummomi ke tserewa daga gidajensu saboda tsananin rashin tsaro.
A cewar kungiyar, mutane da dama sun rasa matsuguni, yara na mutuwa saboda ƙarancin abinci, sannan iyaye, musamman mata, na kallo rayukan yarensu na salwanta a gaban idanuwansu. Amnesty International ta rawaito cewa Kungiyar likitoci ta MSF ta tabbatar da cewa yara 652 sun mutu sakamakon matsanancin rashin abinci cikin watanni shida na farko na bana.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Amnesty International ta nuna damuwa matuƙa kan yadda mutane a ƙananan hukumomi 13 cikin 34 ke fama da hare-hare, garkuwa, kwace amfanin gona da ƙona gidaje, lamarin da ya hana ma’aikatan jin-kai shiga da agajin gaggawa.
Kididdigar UNICEF ta nuna cewa yara sama da 300,000 ba sa zuwa makaranta a Katsina saboda tsaro, tare da karin dubban yara a Dandume, Jibiya, Safana, Batsari, Faskari, Funtua da Kankia da ke fama da matsananciyar rashin lafiya da abinci. Amnesty International ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina su dauki mataki na gaggawa wajen kawo ƙarshen wannan tashin hankali.



