Gwamnatin jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a wasu kananan hukumomi hudu na jihar, bayan hare-hare da suka yi ƙamari cikin sa’o’i 48 da suka gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Laraba, mutane uku sun rasa rayukansu a kauyen Bokungi da ke karamar hukumar Edu, yayin da aka kai hari kan wata coci a garin Eruku da ke karamar hukumar Ekiti, inda mutane biyu suka mutu, sannan aka sace mutum 30.
Wani ganau ya ce maharan sun fara sace mutane huɗu ciki har da ɗan banga, sai daga baya suka kashe manoma biyu da kuma jikkata ɗaya.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta ɗauki matakan tsaro a dukkan makarantu don kare rayuwar ɗalibai da malamai, tare da tabbatar da cewa ba za a bar makarantu cikin haɗari ba.
Matakin ya shafi makarantu a kananan hukumomin Ifelodun, Ekiti, Irepodun, Isin da Oke Ero. Matakin dai ya biyo bayan karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin.



