Rundunar ‘yan sandan Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya ta dakile wani yunƙurin garkuwa da mutane da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su kimanin 30 suka yi a kauyen Guto da ke karamar hukumar Bwari.
A cewar sanarwar da SP Josephine Adeh, kakakin rundunar ‘yan sandan ta aike wa DCL Hausa, ta ce ‘yan sandan sun yi ajalin biyu daga cikin maharan yayin da sauran suka tsere cikin daji.
Sai dai a yayin musayar wuta, wani ɗan sanda ya samu mummunar rauni, inda daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsa a asibitin Bwari.



