Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Bauchi ta dauki matakin ladabtar da wasu manyan ma’aikata huɗu saboda gagarumin cin amanar aiki a yayin gudanar da ayyukansu.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mista Saleh Umar, ya fitar wa manema labarai a Bauchi ranar Juma’a.
Umar ya ce wannan mataki da aka dauka yayin zaman majalisar hukumar, na daga cikin ƙoƙarin da ake yi domin tsaftace harkokin aikin gwamnati a jihar.
Ya bayyana sunayen ma’aikatan da abin ya shafa kamar haka: Garba Hussaini, Darakta (Ilimi) kuma tsohon Provost; Haruna Umar, Mataimakin Darakta (Gudanarwa da Harkokin Ma’aikata); Umar Yusuf, Babban Jami’in Gudanarwa – Bursar; da Mohammed Usman, – Cashier; dukkaninsu na aiki ne a Kwalejin Fasahar Kimiyyar Lafiya ta Bill and Melinda Gates da ke Karamar Hukumar Ningi.



