Gwamnatin jihar Adamawa ta umarci dukkan makarantun sakandare masu kwana na gwamnati da masu zaman kansu da su daina kwana nan take, saboda barazanar tsaro da ta kai ga sace dalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kwamishinan ilimi na jihar, Dr Umar Pella ya ce Gwamna Ahmadu Fintiri ya dauki matakin ne domin kare rayuwar dalibai.
Sanarwar ta bayyana cewa makarantun kwana sun zama babban wurin da ’yan ta’adda ke kai hari, don haka dukkan makarantu za su koma tsarin jeka-ka-dawo ba tare da bata lokaci ba. An umarci dukkan shugabannin makarantu da masu makarantu su aiwatar da wannan sauyi cikin gaggawa.
Hakan na faruwa ne a lokacin da jihohi da dama irin su Kwara, Filato, Katsina da Neja suka rufe makarantu saboda tashin hankali, yayin da Taraba ma ta umurci daina kwana. A lokaci guda.



