Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu na firamare da sakandare bayan sace daliban makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a Agwara.
Wannan na cikin sanarwar da aka fitar bayan taron tsaro da Gwamna Umar Bago ya yi da shugabannin hukumomin tsaro, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bologi Ibrahim, ya bayyana.
Gwamnan ya ce makarantun boko, Islamiyoyi da kwalejojin tarayya ciki har da FGC Minna, duk sun shiga jerin makarantun da aka rufe, sai dai matakin bai shafi manyan makarantu ba face waɗanda ke yankunan da aka ayyana masu hadari a Neja ta Arewa da Gabas.
Bago ya kuma jaddada cewa gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro wajen ceto daliban, inda ake ci-gaba da lissafi domin tantance adadin waɗanda aka sace.



