Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu da dalibai saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kwamishinar ilimi ta jihar, Dr Augustina Godwin, wadda ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari, don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Umarnin ya zo ne a rana guda bayan ’yan ta’adda sun sace dalibai daga makarantar St. Mary a Papiri, Neja, yayin da kusan mako guda da aka yi garkuwa da dalibai 25 a Maga, jihar Kebbi. Lamarin da ya ƙara nuna tabarbarewar tsaro a makarantun Arewacin Nijeriya.



