Dalibai 50 daga cikin waɗanda aka sace a makarantar St. Mary’s Secondary and Primary School da ke Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja sun tsere daga hannun ’yan bindiga kuma sun koma gidajensu lafiya.
A cewar shugaban Kungiyar Kiristoci Nijeriya reshen jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, waɗannan daliban sun kuɓuta ne a ranar Asabar kuma aka haɗa su da iyalansu, kamar yadda sanarwar sakatariyarsa ta bayyana a ranar Lahadi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rev. Yohanna ya ce makarantar na da ɗalibai 430 a aji na firamare, inda 377 suke na kwana. Ya ce yanzu haka, bayan waɗanda suka tsere, dalibai 236, 14 na sakandare da ma’aikata 12 na nan a hannun ’yan bindiga, yayin da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin ceto su.



