Rundunar Sojin Najeriya ta ce barin al’ummomi su kare kansu daga maƙiya ba ya magance rikice-rikicen da faruwa a jihar Filato, illa ƙara tsananta su.
Babban daraktan hulɗar sojoji da fararen hula, Manjo Janar MA Etsy-Ndagi, ya bayyana haka ne a Jos, yana mai cewa tsarin bai taba haifar da da mai ido ba.
A cewarsa, rikicin manoma da makiyaya ya koma salo na hare-hare da ramuwar gayya, inda kowane ɓangare ke zargin ɗaya da farauta ko lalata dukiya.
Hakazalika ya ce dole ne a kwace dukkan makamai kowane iri domin a sami zaman lafiya mai ɗorewa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Etsy-Ndagi ya jaddada cewa sojoji ba sa goyon bayan al’ummomi su ɗauki doka a hannunsu, sai dai suna kare garuruwan da ke fuskantar tashin hankali. Ya kuma yi kira ga mazauna Filato da su zauna lafiya su kuma ba ƙungiyoyin tsaro hadin kai.



