Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya ce shawarar da ya ɗauka na komawa jam’iyyar APC ta samo asali ne daga bukatar kare muradun mutanensa, ya bayyana haka ne a wani biki na raya al’adun kabilar Margi da aka yi a Jimeta, Jihar Adamawa a ranar Asabar.
Kefas, wanda ya dage bikin shigarsa APC saboda sace ’yan mata a Kebbi, ya ce taron ba na siyasa ba ne, sai dai na ɗaukaka al’adun Margi inda ya bayyana cewa duk wani sabani tsakaninsa da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya samo asali ne daga matakin da ya ɗauka na sauya sheƙa domin muradun jama’ar Taraba.
A cewarsa, kabilar Margi sun taru ne domin duba tarihinsu da makomarsu, yana mai cewa duk da sabanin siyasa, Fintiri ɗa Margi ne na gari kuma mai son haɗin kai, kuma yana da tabbacin daga ƙarshe zai yarda cewa matakin da ya dauka zai yi amfani ga jama’a.
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda ya halarci taron, ya soki yadda siyasar ƙasar ke sauya salo zuwa tsarin jam’iyya daya, yana mai gargadin cewa hakan ba zai haifar da da mai ido ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



