Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin da tsohon gwamna jihar, Nasir El-Rufa’i ya yi a Channels TV cewa gwamnatin Uba Sani ta biya ’yan bindiga Naira biliyan 1, tana mai cewa maganar ba ta da tushe balle makama. Wannan na cikin sanarwar da ma’aikatar tsaro ta cikin gida ta fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya riga ya ƙaryata irin waɗannan kalamai tun da, yana tabbatar da cewa babu wata gwamnati da ke biyan kuɗi ga masu laifi. Ta kuma ce El-Rufa’i bai taɓa gabatar da takarda ko wata hujja da ke jaddada zancensa ba.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa gwamnatin Uba Sani na aiwatar da dabarar tsaro mai dogaro da al’umma, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya, ba ta kuma taɓa tattaunawa ko biyan kuɗi ga ’yan bindiga ba.
Sanarwar ta ce idan El-Rufa’i na da hujja kamar na bayanan banki ko takardun gwamnati ya fito da su cikin sati guda, in ba haka ba a ɗauki matakin doka. Ta ƙara da cewa gwamnatin Kaduna ba za ta bari siyasa ta rikita ci-gaban tsaro da ta fara yin nasara a kai ba.



