DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnonin Arewacin Nijeriya sun karbi Naira biliyan 56 a cikin wata 9 don inganta tsaro

-

Wani bincike da jaridar Punch ta ruwaito ya nuna jihohi 14 na Arewacin Nijeriya sun karbi Naira Biliyan 56 domin inganta tsaro a cikin watanni tara na 2025, duk da cewa hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane sun ƙara tsananta a jihohin Neja, Kebbi, Kano da Kwara.

Daga cikin manya-manyan hare-haren akwai sace dalibai 315 da malamai 13 a Papiri, tare da ƙarin mutane 26 a Kebbi da 24 a Shiroro.

Google search engine

Yawaitar hare-haren ya tayar da hankulan jama’a, musamman bayan an sake yin garkuwa da mata masu juna biyu, yara da masu shayarwa a Kwara da Kano cikin mako guda. Lamarin da ya tilasta shugaba Tinubu ayyana dokar gaggawa kan tsaro tare da umartar daukar karin jami’an tsaro 20,000.

Duk da cewa kuɗin inganta tsaro na nufin daukar matakan gaggawa da tattara bayanan sirri, jama’a na zargin ana batar da kudaden ne kawai ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.

Binciken ya nuna jihohin sun kashe kusan rabin Naira Biliyan 101 da suka ware a 2025, amma hare-hare na ci-gaba da yi wa Arewa barazana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar Tarayyar Turai ta yi Allah-wadai da haramta biza da Amurka ta yi wa wasu Turawa

Tarayyar Turai, tare da ƙasashen Faransa da Jamus, sun yi kakkausar suka ga matakin Amurka na haramta biza ga wasu ’yan Turai da ke yaki...

Shugaba Tinubu ya yi kira ga hadin kai da hakuri a tsakanin addinai a cikin sakon taya murnar bikin Kirsimeti

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi haɗin kai, juriya da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, yana mai cewa...

Mafi Shahara