Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun halaka ’yan ta’adda da dama, sun kama mutane 57 da ake zargi, tare da ceto mutane 45 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda, a cewar daraktan yaɗa labaran tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja.
A cewarsa, dakarun sun kuma kwato makamai, motoci da harsasai, tare da rusa sansanonin ’yan ta’adda a yankuna daban-daban kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai ta kashe ’yan ta’adda da dama, ta kama mutane 11 da ake zargi da taimaka musu, ta kuma kubutar da fasinjoji 8 da aka sace. Jiragen yakin sama sun yi luguden wuta a dajin Sambisa, inda suka halaka ’yan ta’adda tare da lalata wuraren boye makamansu.
Haka kuma, dakarun Operation FASAN YAMMA, sun hallaka ’yan bindiga da dama, tare da kama 15, da kuma ceto mutane 13 a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, Katsina, Kaduna da Neja. Dakarun sun kuma kwato makamai, motocci, dabbobi da kuma wani dillalin makamai dauke da Naira miliyan 4 da makamai irin na soji.



