Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen Kudancin Kaduna ta bayyana aniyar haɗa kai da hukumomin tsaro domin magance matsalar tsaro a yankin.
Wannan kudiri ya fito ne a taron da aka gudanar a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a, a ranar Lahadi.
Shugaban MACBAN na yankin Kudancin Kaduna, Alhaji Mato Yahaya, ya ce lokaci ya yi da za a nemo mafita, tare da yin kira ga shugabanni su faɗi gaskiya kuma su gabatar da shawarwari masu amfani domin magance matsalolin yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin makiyaya da sauran al’umma.
A nasa jawabin, shugaban MACBAN na jihar Kaduna, Alhaji Abdulhamid Albarka, ya ce an shirya taron ne domin tattara ra’ayoyin jagororin Fulani na ƙananun hukumomi, sannan a mika su ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.



