Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya ce shi ne babban jami’in Kirista mafi matsayi a gwamnatin Nijeriya, yana mai danganta nasararsa ta siyasa ga “ni’imar Allah ta musamman.”
Akpabio ya faɗi haka ne a lokacin bude wani wajen ibada na Regina Coeli a Uyo, kamar yadda sanarwar mai taimaka masa, Jackson Udom, ta tabbatar.
A cewarsa, tafiyarsa daga rashin sani zuwa zama mutum na uku a jagorancin ƙasa hujja ce ta yadda Allah ke ɗaukaka wandanda ya nufa. Ya ce duk Kirista na iya samun irin wannan tagomashi muddin ya tanadi kansa don albarkar Ubangiji.
Ya kuma jaddada muhimmancin aikin ikilisiya, yana cewa ko gudummawar da ta kai kobo goma ga aikin gina coci tana da lada mai girma.
Har ila yau, jaridar Punch ta ruwaito Akpabio ya bayyana shirinsa na gina sabon wurin ibada a cikin majalisar dokoki na Abuja.



