Sojojin Operation MESA ƙarƙashin Birget ta 3 sun ceto mutane bakwai da ’yan bindiga suka sace a Tsanyawa, bayan samun kiran gaggawa daga Yankamaye Cikin Gari a daren Juma’a.
Jami’an tsaro sun isa wurin cikin gaggawa tare da rundunar sojin sama da ’yan sanda, suka yi artabu da maharan inda suka kubutar da wadanda aka sace.
Sanarwar da Kyaftin Babatunde Zubairu ya fitar ta ce maharan sun kashe wata mata mai shekaru 60 kafin isowar sojoji. Bayan musayar wuta, rundunar ta bi sawun ’yan bindigar zuwa hanyar Rimaye, inda suka sake cakumar juna har maharan suka tsere suka bar mutanen da suka sace.
Sai dai mutum huɗu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ba a same su ba tukuna, yayin da rahoton ya ce ’yan bindigar sun tsere zuwa yankin Kankiya a jihar Katsina. Jami’an tsaro suna ci-gaba da bin diddigin motsin su domin gano su.
Kwamandan Birget ta 3 ya yaba da jajircewar sojoji, yana kuma kira ga jama’a da su cigaba da bayar da sahihan bayanai don ƙarfafa yaki da ’yan bindiga a yankunan kan iyaka.



