Rundunar sojin saman Nijeriya sun samu manyan nasarori a ayyukan su na kai farmaki, inda suka tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda a jihar Katsina sannan suka dakile hare-haren ‘yan tada kayar baya a Chibok, Borno.
Wannan ya biyo bayan amfani da bayanan leken asiri da ya bai wa jiragen yakin damar kai farmaki daidai-wa-daida kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A Katsina, farmaki na farko da aka kai da karfe 6 na safe ya hallaka masu ta’addanci da suka yi yunkurin tserewa daga sansanonin su a Kankara, Faskari da Malumfashi, yayin da farmaki na biyu a Danfako ya rusa cibiyoyin kayan aiki da sansanonin masu ta’addanci. Wannan ya raunana kungiyar sosai kuma ya hana su motsi cikin ‘yanci a Yammacin Arewacin Nijeriya
A Borno kuwa, jiragen saman sun tallafa wa sojojin Birget na 28 yayin da ‘yan ta’adda suka kai hari mai fadi a Chibok.
An kai farmaki hudu kan ‘yan ta’addan da ke tattara kansu ko ja da baya, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da hana su sake shirya hari. Wannan hadin gwiwar aiki na kasa da sama ya tabbatar da tsaron mazauna yankin.



