DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun sace matafiya a babban titin jihar Kogi

-

Wasu ’yan bindiga sun tare motoci a kan hanyar Isanlu–Makutu–Idofin da ke Yagba ta Gabas a jihar Kogi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

Mazauna wajen sun ce maharan sun kafa shinge na tsawon sa’o’i, inda motoci uku suka faɗa tarkonsu, kuma mutum ɗaya kacal ya kuɓuta.

Google search engine

Kamar yadda mazauna yankin suka shaida, jami’an soji da ’yan sa-kai sun bi sawun maharan daga baya suka kuma yi musayar wuta da su, lamarin da ya kai ga kubutar da wasu daga cikin fasinjojin da aka sace.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP William Aya, ya ce mutum biyu aka sace yayin da wani Raji Adesukami ya tsere, kuma an tura tawaga ta musamman domin ceto sauran.

Wata majiya ta rundunar soji ta bayyana cewa sojojin Birget ta 12 sun ceto mutane biyar a yayin wani samame da suka kai a yankin Isanlu–Egbe a ranar 29 ga Nuwamba, bayan wasu hare-haren sace mutane da suka afku a yankin.

A halin yanzu, Gwamna Usman Ododo ya ce za a kai farmaki kai tsaye cikin dazukan da ’yan bindiga ke ɓoyewa domin kare rayukan jama’ar jihar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara