Hadimin shugaba Tinubu na Nijeriya Daniel Bwala ya bayyana cewa gwamnati na daf da kwarmata sunayen masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.
Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da ‘Television Continental’ a ranar Lahadi, yana mai bayyana cewa tuni gwamnatin Tinubu ta fara daukar tsauraran matakai kan lamuran tsaro a kasar, wadanda za su bayyana ga ‘yan Nijeriya nan ba da jimawa ba.
Jaridar Punch ta ruwaito Hadimin shugaban na cewa gwamnatin ta kusa fallasa sunayen masu daukar nauyin duk wani nau’i na tashin hankali da ake fama da shi a sassan kasar.
Kazalika ya jaddada bukatar samar da hadin kai a tsakanin kasashe musamman masu makwabtaka da juna wajen yakar matsalar tsaro.



