Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana cewa akalla mutane 17,000 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a jihohin Kaduna da Katsina cikin shekarar 2025.
Wannan bayani ya fito daga bakin shugaban ofishin hukumar na jihar Kaduna Suleiman Muhammad, yayin gudanar da aikin bibiyar yankunan da lamarin ya shafa.
A cewar Suleiman, irin asarar da aka samu ta tilasta hukumar yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen gudanar da ayyukan ceto da kuma na tallafi don rage radadi.
Kazalika ya bayyana samun rahoton asarar rai a jihar Katsina sakamakon ambaliyar, sai dai ba a samu asarar rai a Kaduna ba.



