Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da shugabannin jam’iyyar ADC na jihohin kasar.
Atiku Abubakar ya tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa daukacin shugabannin sun kawo masa ziyara ne don yi masa barka da shiga ADC a hukumance.
Yayin tattaunawar, Atiku ya bukaci a samar da kyakkyawan hadin kai a jam’iyyar don tunkarar abin da ke gabansu, yana mai cewa babu bukatar bata lokaci a daidai wannan lokaci.



