Gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya sun bukaci a dakatar da hakar ma’adanai a yankin na tsawon watanni shida, suna bayyana shi a matsayin babban dalilin ta’azzarar matsalolin tsaro a yankin.
Wannan ya biyo bayan wani taro da suka gudanar a ranar Litinin, domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar.
Kazalika sun bayyana shirin bude asusu wanda za su tara Naira biliyan 228 don inganta yakinsu da matsalar.
Karkashin shirin dai, kowace jiha da kananan hukumominta za su rika bayar da Naira biliyan 1 a kowane wata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



