Gwamnatin Nijeriya ta amince da bai wa dan adawar Guinea-Bissau Fernando Dias da Costa mafaka, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Wannan mataki dai na kunshe ne cikin wakikar da ministan harkokin wajen Nijeriya Ambasada Yusuf Tuggar ya aike wa da shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.
A cewar gwamnatin Nijeriya, daukar matakin zai taimaka wajen bai wa Fernando Dias tsaro, musamman yadda ya bayyana cewa yana fuskantar barazana tun bayan juyin mulkin.
A makon da ya gabata ne dai sojoji suka sanar da karbe iko da mulkin kasar ta Guinea-Bissau, daidai lokacin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana, lamarin da gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da shi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Kazalika tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, wanda ya kasance mai sa ido a zaben kasar ya nuna shakku kan juyin mulkin, yana mai zargin cewa hambararren shugaba Oumarou Sissoco Embalo ne ya kitsa shi.



