An samu tashin hankali a Unguwan Nungu da ke mazabar Bokana a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna, bayan da ‘yan bindiga suka sace mutane 11 a lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.
Daily Trust ta ruwaito mazauna yankin na tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutanen cikin dazuka, ba tare da an san ina suka nufa ba.
Kazalika wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun nemi a biya su kudin fansa miliyan 11 kafin su sako mutanen da suka sace.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya ta’azzara fargaba a zukatan mazauna yankin da kuma masu makwabtaka da su.



