Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fasalin dokokin cire kuɗi daga bankuna kan sabon tsarin da zai fara aiki daga watan Janairun 2026.
Babban bankin ya bayyana cewa an ƙirƙiri tsare-tsaren cirar kuɗi da dama a baya bisa la’akari da yanayin da ake ciki, dalili kenan da aka bijiro da wannan sabon tsarin.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 2 ga watan Disamban 2025, CBN ya ce daga cikin manufofin sauyin akwai takaita kashe kudi wajen gudanar da harkoki, ƙarfafa tsaro, da kuma dakile barazanar almundahanar kuɗaɗe.
Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, mutane za su iya cire kuɗi har zuwa Naira 500,000 a kowane mako, yayin da kamfanoni za su iya cire har zuwa Naira miliyan 5, kamar yadda Channels TV ya wallafa.



