Hadimin shugaban Nijeriya Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta taɓa yin tattaunawa da ’yan ta’adda ko biyan su kuɗin fansa ba, duk da jita-jitar da ke yawo game da sakin yara ‘yan makaranta da aka sace.
A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Bwala ya bayyana cewa a wasu gwamnatoci da suka gabata, hukumomi na shiga tattaunawa da’ yan bindiga domin kare rayukan ’yan ƙasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai ya ce gwamnatin Tinubu ba ta amince da daukar hanyar ba, domin a cewarsa hakan na kara karfafar ‘yan ta’adda ne a fakaice.



