Tsohon babban hafsan sojin kasan Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (rtd), ya ce maganganun da ke cewa Nijeriya na dab da rushewa ba su da tushe.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana hakan a matsayin kalaman da ba su dace ba kuma ba su yi la’akari da tarihin dorewar kasar ba.
Buratai ya ce Nijeriya ta sha tsira daga rikice-rikicen siyasa, matsin tattalin arziki da kalubalen tsaro da ka iya karya wasu kasashe.
A cewarsa, sabon salo na shugabanci mai kishin kasa na fitowa a gwamnati da bangarori daban-daban.



