Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 861 na shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin Jihar a Gusau, yana mai cewa wannan kasafi taswira ce ta sauyi, domin a cewarsa, kasafin ya kunshi kuɗin ayyukan ci-gaba na N714bn wanda ya kunshi kaso 83 da kuɗin gudanarwa na kusan N147bn (kaso 17).
Dauda ya ce gwamnatinsa, wadda aka zaɓa a kan alkawarin ceto, gyara da farfaɗo da jihar, ta yi aiki tukuru don farfaɗo da muhimman bangarori da kuma gina tubalin ci-gaba mai ɗorewa.
Hakazalika, Gwamna Lawal ya kara da cewa mutanen Zamfara yanzu suna ganin haske da ci-gaba, yayin da kasafin 2026 wanda ya kira kasafin tabbatar da daidaito da ci-gaba ke nufin zurfafa nasarorin da aka cimma ta hanyar shirin Six-Point Rescue Agenda.
Kasafin ya ba da fifiko ga tsaro, inganta aikin noma, sabunta fannin kiwon lafiya, faɗaɗa ilimi, gina manyan ayyukan raya ƙasa, da kuma ƙarfafa matasa, mata da marasa galihu, tare da tabbatar da cewa babu wani yanki ko al’umma da za a bari a baya.



