Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana cewa dakarun da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar sun ceto mutane 318 da aka yi garkuwa da su a watan Nuwamba, tare da kama wasu 74 da ake zargi da ta’addanci da fataucin mai da sauran laifuka.
A cewar Daraktan yada labarai na tsaro, Maj. Janar Michael Onoja, wanda ya yi jawabi an Abuja, ya ce a wannan watan kuma ’yan ta’adda 69 da iyalansu sun mika wuya a Arewa maso Gabas.
Hedkwatan tsaron ta ce dakarun sun kuma dakile satar mai da kimar ta kai sama da N217m, tare da rushe wuraren tace mai na bogi 16 da gano lita 201,700 na ɗanyen mai da lita 88,177 na dizal.
Onoja ya kuma yaba wa dakarun bisa ƙoƙarinsu, tare da roƙon jama’a da su ci-gaba da ba da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro.



