Wani alkali da ke wata kotun majistire a jihar Gombe, Mohammed Kumo, ya gurfana a gaban kotu kan zargin sa da karbar cin hanci da kuma tatsar kudade.
Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ce ta gurfanar da alkalin, kamar yadda yake a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar ta ce an maka shi ne gaban mai shari’a H.H Kereng da ke babbar kotun Gombe, ana tuhumar sa da aikata laifuka uku, kamar yadda EFCC reshen jihar ta mika.
Sai dai wanda ake kara ya musanta aikata laifukan, dalili kenan da mai shari’a ya bayar da belinsa, tare da dage zaman shari’ar zuwa ranakun 13 da 14 ga watan Janairun 2026, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



