Wasu limaman coci sun yi watsi da zargin Amurka da ke cewa ana gudanar da kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya.
Limaman sun mayar da martani ne kan maganganun shugaban Amurka Donald Trump, wanda da fari ya yi barazanar daukar matakin soji a kan kasar.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Bishop Timothy Cheren, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa akwai kisan kiyashi da gwamnati ke daukar nauyi ko kuma dauke kai daga haka.
Cheren ya yabawa kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen yaki da matsalar tsaro, tare da mika kira ga ‘yan Nijeriya da su mara wa kokarin da ake yi na kawo karshen ta’addanci a Nijeriya, kamar Daily Trust ta ruwaito.



