Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa da yadda ake kashe makuden kudade a fannin tsaro, yana mai cewa gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan 100 a fannin cikin shekarar 2025 da muke bankwana da ita.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Sarkin Uba, Ali Ibn Mamza a fadarsa da ke garin Uba, karamar hukumar Askira/Uba a jihar ta Borno.
Zulum ya ce dalilin ziyarar ita ce duba halin da tsaro ke ciki a yankin, yana nuna damuwa da yadda matsalar tsaron ke sa a yi watsi da ayyukan tituna.
Sai dai ya sha alwashin cewa nan ba da jimawa ba, za a ci gaba da gudanar da ayyukan titunan, baya ga manyan makarantu da kuma cibiyoyin ilimin na’ura mai kwakwalwa.



