Attajirin Amurka kuma guda cikin tsofaffin masu mallakar kungiyoyin wasanni, Tom Hicks, ya rasu yana da shekaru 79.
Hicks ya rasu ne a ranar Asabar a birnin Dallas, kamar yadda kamfaninsa Hicks Holdings LLC ya tabbatar a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Liverpool.
Rahoton da jaridar Punch ta ruwaito ya ce Hicks ya shahara a harkar kasuwancin wasanni a Amurka.
Ya mallaki kulob din Dallas Stars na NHL daga 1995 zuwa 2011, lokacin da suka lashe Stanley Cup a 1999.
Haka kuma ya kasance mai mallakar Texas Rangers na Major League Baseball daga 1998 zuwa 2010, inda kungiyar ta kai ga buga gasar World Series.
A 2007, Hicks ya saye rabin hannun jari a Liverpool FC, sai dai zamaninsa a kungiyar ya cika da rigingimu kan kudi da tafiyar da kulob din, wanda daga baya ya kai ga sayar da shi.



