Wata kungiyar fararen hula wadda ke gudanar da harkokin da suka shafi addini mai suna ‘Independent Hajj Reporters’ ta sake mika kira ga hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON, da hukumomin jin dadin Alhazai na jihohi su mayar da rarar kudaden da mahajjata sama da dubu 40 suka biya a yayin aikin hajjin 2025.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Ibrahim Muhammad, ta ce kowane Alhaji cikin wadanda suka biya kudaden da suka yi yawa, na bin abin da ya kama daga Naira 400,000 zuwa 437,000, dogaro da bambancin da ke tsakanin farashin kasuwar canjin kudade da kuma yadda suka biya a lokacin aikin hajjin na 2025.
A cewar kungiyar, kafin wannan lokaci hukumar NAHCON ta bayyana yiwuwar mayar wa da Alhazan kudaden su bayan kammala aikin 2025, tana mai jaddada bukatar yin hakan cikin gaggawa kafin a fara aikin hajjin 2026.



