Jam’iyyar APC ta yi kira da a kara hakuri da kuma bai wa jami’an tsaro goyon baya yayin da suke kokarin ceto yaran da aka sace da kuma yaki da matsalar tsaro a fadin Nijeriya.
A wata hira da Channels TV, kakakin jam’iyyar, Felix Morka, ya ce kare rayuwar yaran da aka sace shi ne babban abin da gwamnati ke muradi, don haka dole jami’an tsaro su yi aiki cikin taka tsantsan.
Ya ce ayyukan ceto yara na bukatar kulawa ta musamman saboda kuskure kadan na iya jefa su cikin hatsari. Morka ya roki ‘yan Najeriya da su nuna hakuri da fahimta ga kokarin rundunonin tsaro.
Rahoton jaridar Punch ya ce Morka ya kuma yaba da jajircewar sojoji da sauran jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu don kare kasar.



