Wani hadimin shugaban Faransa ya shaida wa gidan talabijin na France24 cewa Shugaba Emmanuel Macron ya tallafa wajen dakile yunkurin juyin mulkin da aka so yi a Jamhuriyar Benin.
Gidan talabijin din ya ruwaito hadimin Macron din na cewa mai gidansa ya tattauna da shugabannin ECOWAS da suka hada da Najeriya da Saliyo kafin samar da kayan aikin da ake bukata kafin samun damar kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyi9n mulkin. Hadimin shugaban Faransa da ya bukaci kada gidan talabijin na France24 ya bayyana sunansa ya ce tallafin da Faransa ta bayra ga sojojin Jamhuriyar Benin sun hada da bayanan sirri domin tabbatar da cewa juyin mulkin da aka so yi bai yi nasara ba.



