Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatin jiharsa za ta ba kowane ɗan gudun hijira ɗan Borno da yake a Kamaru N500,000 idan ya amince ya koma gida.
Zulum ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ‘yan gudun hijira a sansanin Minawao, da ke yankin Arewa ta Gabashin Kamaru.
Jaridar Punch ta ambato shi na cewa samar da cikakken tsaro a yankunan da za su koma, musamman bayan manyan hare-haren soji da ƙarfafa tsaron farar hula a Gwoza da sauran yankuna na jihar.



