Hukumar ICPC ta bayyana cewa matsalar rashawa a Najeriya ta yi zurfi matuka, inda ta ce idan aka aiwatar da dokoki yadda ya kamata, kusan kashi 80% na ‘yan kasa na iya fuskantar hukunci.
Bayanin hakan ya fito ne daga Kwamishinan hukumar ICPC na Kaduna, Sakaba Ishaku, a taron horaswa kan inganta gaskiya da rikon amana a kananan hukumomi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi cewa rashawa ta shafi kusan dukkan bangarorin gwamnati da al’umma, kuma tana haifar da tasirin da ya hada da karancin albarkatu, karuwar talauci, da tsaikon cigaba ga kasa.
Ya kuma jaddada cewa rashin ingantacciyar kulawa da amana yana lalata kudaden jama’a, tare da yin kira ga shugabannin kananan hukumomi su kauce wa abin da zai munana tarihinsu.



