Jami’an ‘Yan Sandan Birnin Tarayya sun kama wani mutum mai shekaru 32, Ahmed Abubakar, bisa zargin ƙoƙarin sayar da harsasai guda 1,000 ga ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na FCT, Miller G. Dantawaye, ya ce an kama Ahmed ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma a Unguwar Dodo, Gwagwalada, bayan samun sahihan bayanai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Bincike ya nuna cewa Ahmed yana hulɗa da wani mai suna Yusuf Mohammed, kuma an aika shi da wannan aikin ne ta hannun ƙanin sa, Ahmed Yakubu, wanda ake kyautata zaton yana da hannu a harkar laifuka kuma har yanzu ba a kama shi ba.
An ce ana ƙoƙarin cafke Yakubu da kuma rushe wannan hanyar laifi baki ɗaya, yayin da Ahmed ke hannun ‘yan sanda a yanzu.



