Matatar Dangote ta sake rage farashin fetur a matakin ex-depot daga N828 zuwa N699 kan lita, matakin da ya saukar da farashin ƙasa da N800 a karon farko cikin watanni. Ragewar ta kai N125 kan lita, wadda ke nuna faduwar farashi da kusan kashi 15.58.
Kamar yadda bayanan Petroleumprice.ng suka nuna a ranar Juma’a, sabon farashin ya fara aiki ne tun 11 ga Disamba, 2025.
Wani mai magana da yawun Dangote, Tony Chiejina, ya tabbatar da sauyin farashin, yana mai cewa wannan shi ne sauyi na 20 da matatar ta yi a bana kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyoyi sun ce an yi wannan ragin ne domin rage kuɗin sufuri gabanin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, lokacin da ’yan Nijeriya ke yawan tafiye-tafiye don haduwa da iyalai.



