Wani matashi mai shekaru 25, mai suna Adamu Abdullahi, ya rasa ransa bayan da wasu fusatattun jama’a suka yi masa dukan tsiya har lahira a garin Suleja, ta jihar Neja, bisa zargin da aka yi masa na soka wa mahaifiyarsa wuka.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, bayan wata takaddama da ta barke tsakanin matashin da mahaifiyarsa mai shekaru 45, Hauwa Sanusi, kan rabon gadon mahaifinsa marigayi. Rahotanni sun ce mahaifiyar ta rike rabon gadon ne domin gudun kada a almubazzarance shi.
Wata majiya ta shaida cewa matashin, wanda ya dade baya zama a Suleja, ya dawo garin ne ba tare da sanin jama’a ba, inda ya kai wa mahaifiyarsa hari da wuka sau da dama.
Ihun da matar ta yi ne ya ja hankalin makwabta, suka kamo matashin yayin da yake kokarin tserewa, inda daga bisani wasu matasa suka yi masa dukan tsiya kafin ‘yan sanda su iso. An kuma tabbatar da cewa matar da aka kai wa harin ita ce mahaifiyarsa ta jini.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayyana dalilin rikicin ba.



