Tsohon ɗan majalisar dattawa daga jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Ayodele Arise, ya bukaci Shugaba Tinubu da ya yi la’akari da amfani da karfin soji kan ƙasar Burkina Faso domin ganin an sako sojojin Nijeriya da ake tsare da su a can.
Arise ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce duk da cewa sojojin Nijeriya na fuskantar manyan ƙalubale a gida sakamakon ta’addanci da ‘yan bindiga, bai kamata a kawar da zaɓin daukar matakin soja kan Burkina Faso ba.
Ya tuno da wani misali na tarihi, inda ya ambaci harin da Isra’ila ta kai Entebbe a Uganda a 1976, yana mai cewa irin wannan mataki na iya tilasta wa shugabannin Burkina Faso sake tunani. A cewarsa, Nijeriya na bukatar ta nuna wa makwabtanta cewa duk da kyakkyawar mu’amala, ba za a yarda a raina ƙasar ba.
Sanatan, wanda ya taba wakiltar Ekiti ta Arewa a majalisar dattawa, ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin soja da aka dauka kwanan nan a Jamhuriyar Benin domin dakile yunkurin juyin mulki.



