Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fara shirin rajista, tantancewa da kuma jawo sabbin mambobi na tsawon kwanaki 90 a fadin Nijeriya, domin karfafa jam’iyyar daga tushe.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce an dauki matakin ne bayan kammala taron kwamitin gudanarwa na kasa da aka gudanar a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2025, bisa tanadin kundin tsarin jam’iyyar.
ADC ta kuma sanar da shirinta na gudanar da tarukan zabe a matakin rumfunan zabe, mazabu da kananan hukumomi daga ranar 20 zuwa 27 ga Janairu, 2026, kafin babban taron kasa da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairu, 2026 a Abuja.
Jam’iyyar ta ce wannan shiri na da matukar muhimmanci wajen karfafa hadin kan mambobi da tsari a fadin kasa.



