Kungiyar dattawan Arewa ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta soke yarjejeniyar fahimta da Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (FIRS) ta kulla da hukumar haraji ta Faransa,, tana mai cewa yarjejeniyar na barazana ga ikon tattalin arziki da tsaron kasa.
A wata budaddiyar wasika da ta aikewa gwamnatin Nijeriya, majalisar dattawa da majalisar wakilai, kungiyar ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “hadari ga bayanan haraji,” wadda za ta iya bai wa wata kasa ikon mallakar muhimman bayanan tattalin arzikin Nijeriya.
Wasikar wadda mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere ya sanya wa hannu, ta ce yarjejeniyar ta wuce hadin gwiwar fasaha kawai, tana mai gargadin cewa tana zama wata hanya kai tsaye da ba ta da kariya zuwa cibiyar tsarin haraji na Nijeriya, tare da mika bayanai masu matukar muhimmanci ga ikon wata kasa ta waje.



