Kungiyar kare hakkin dan-adam da tabbatar da gaskiya (SERAP) ta yi barazanar shigar da kara kan Ministan Shari’a da babban Lauyan Nijeriya, Mista Lateef Fagbemi, SAN, saboda rashin aiwatar da hukuncin kotu kan zargin almundahana na Naira tiriliyan 6 da ake tuhumar Hukumar Ci Gaban Niger Delta (NDDC) da yi.
A cikin wata wasika da aka sanya ranar 13 ga Disamba, kungiyar ta umurci Fagbemi da ya aiwatar da hukuncin da Alh. Justice Gladys Olotu ta bayar a ranar 10 ga Nuwamba, 2025.
Kotun ta umurci Fagbemi da Shugaba Bola Tinubu da su “fitar da sunayen wadanda ake zargi da almundahana a cikin Naira tiriliyan 6 da aka ware don aiwatar da ayyuka 13,777 da aka dakatar da su da kuma gudanar da NDDC tsakanin 2000 da 2019.”
Hukuncin ya kuma umarci wallafa “rahoton binciken kudi na NDDC da aka mika ga gwamnatin tarayya a ranar 2 ga Satumba, 2021.” SERAP ta bayyana cewa rashin aiwatar da hukuncin wulakanci ne ga tsarin shari’a da doka a kasar.
Kungiyar ta gargadi cewa ci-gaba da kin aiwatar da hukuncin na iya sanya Fagbemi da Shugaba Tinubu fuskantar daukar alhakin kansu.



